Kotun ICC ta zo ƙarshen shari'ar Thomas Lubanga
July 10, 2012Kotun duniya da ke hukunta masu laifukan yaƙi ta ɗaure tsohon shugaban 'yan tawayen Janhuriyar Demokaraɗiyyar Kongo hukunci na tsawon shekaru 14 a gidan fursuna.
Kotun ta samu Thomas Lubanga da laifukan ɗiban yara aikin soja, cikin yankin Ituri abun da ya kai ga yaƙin basasan ƙasar Janhuriyar Demokaradiyyar Kongo da ya kawo ƙarshe a shekara ta 2003, Kuma alƙalin da ya jagaronci zaman Andrian Fulford ya bayyana wannan hukuncin da aka yankewa Lubanga, tsohon madugun 'yan tawayen ƙasar ta Janhuriyar Demokaradiyyar Kongo:
Bisa hukuncin masu rinjaye, Mr Lubanga an ɗaure shi na tsawon shekaru 14 a gidan kurkuku, kuma farawa daga lokacin da kotu ta cafke shi, ranar 16 ga watan Maris shekara ta 2006, za a kwashe daga ciki.
Wannan shine hukuncin kotun na farko tun bayan kafa ta fiye da shekaru 10 da suka gabata, kuma ƙarƙashin dokokin da suka kafa kotun tana iya ɗaure mai laifi har na tsawon shekaru 30 ko kuma ɗaurin rai da rai. Masu gabatar da ƙara sun nemi yanke hukunci mai tsauri kan Lubanga ɗan shekaru 51 da haihuwa.
Amma duk da hukuncin Lubanga ya musanta aikatan laifin ɗaukan yara aikin soja, yayin jawabi a gaban kotun:
Amma abunda ya tabbata shine, ni Thomas Lubanga, ni ko yaushe ina adawa ɗaukan kuma ko yaushe ina wannan adawar.
A cikin nasu martanin ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama na ƙasar ta Janhuriyar Demokaradiyyar Kongo, sun nuna rashin jin daɗin rashin cafke sauran masu laifi, kamar yadda Doli Ibefo ke cewa:
Wannan shari'a ba ta yi ba ganin yadda akwai wasu mutanen da suka tabka ta'asa amma babu abunda ya faru dasu, kamar Bosco Ntaganda, waɗanda ke da laifi Thomas Lubanga.
Amma ƙungiyar tawaye da Lunbanga ya jagoranta, da ta rikiɗe ta zama jam'iyyar siyasa ta UPC, ta ce wannan hukuncin wata dabarar siyasa ce kawai, kamar yadda mataimakin shugaban jam'iyya kuma ɗan majalisar dokoki, Dechuvi Macho ya bayyana:
Yanke hukunci akan mutun na buƙatar gamssasun hujjoji. Amma Thomas Lubanga, babu wannan. Babu wani yaro shaida a matsayin hujja. Masu gabatar da ƙara sun kawo yara na ƙarya waɗanda suka wahala. Babu abunda muka gani illa daurewa ƙarya gindi. Yara na ƙarya, shaidun ƙarya, hujjojin ƙarya, yaran ma babu wanda bai fi shekaru 15 ba.
Masu nazarin abubuwan dake faruwa a ƙasar ta Janhuriyar Demokaraɗiyyar Kongo, sun yi gargaɗin muddun ba a ɗaukin matakan shiga tsakani ba, ƙasar ka iya sake tsunduma cikin yaƙin basasa kamar abun da ya faru shekaru 18 da suka gabata. Inda yanzu haka kimanin mutane 200,000 suka tsere daga gidajensu, sakamakon sabon tashin hankali.
Rohoton Majalisar Dinkin Duniya ya zargi Ruanda da hannu cikin rikicin abun da ta musanta.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi