1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotun ICC za ta yanke hukunci kan masu Ikrarin jihadi a Mali

April 16, 2024

Rahotanni daga birnin Hague na cewa, kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ke Netherlands ta sanya ranar da za ta yanke hukunci kan masu ikrarin jihadin nan 'yan Mali a watan Yunin wannan shekara ta 2024.

Alkalan kotun ICC da ke birnin Haque a lokacin da suke sauraron karar da aka shigar kan  Al Hassan da ake zargi da cin zarafin mata a Mali
Alkalan kotun ICC da ke birnin Haque a lokacin da suke sauraron karar da aka shigar kan Al Hassan da ake zargi da cin zarafin mata a MaliHoto: Eva Plevier/ANP/picture alliance

Babban mai shigar da kara na kotun ICC ya ce mutanen ciki har da Al Hassan wanda ya yi kaurin suna wajen azabtar da mutane da yiwa mata fyade da bautar da su harma da yi musu auren dole ga 'ya'yan kungiyar ta masu ikrarin jihadi a yankin Timbuktu da ke kasar ta Mali.

Karin bayani: Tsageru suna kara kaimi a Mali 

Al Hassan shi ne mutum na biyu daga cikin masu ikrarin jihadin da aka gabatar a kotun ICC kan zargin lalata wasu muhimman wurare na addini da na tarihi da hukumar UNESCO ta ware a matsayin wurare masu matukar muhimmanci.

Karin bayani: ICC: Al Faqi zai biya diyyar hubbaren Timbuktu

Kotun dai ta yanke wa mutum na farko Ahmad Al Faqi Al Mahdi hukuncin daurin shekaru 9 a shekara ta 2016, wanda bayan daukaka kara kotun ta rage daurin zuwa shekara 2 a 2021.