1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun kasa da kasa ta tabbatar da laifin Charles Taylor

April 26, 2012

Kotu a Hague, ta sami tsohon shugaban Liberia da laifukan yaki

Hoto: AP

A yau ne kotun ƙasa da ƙasa da ke birnin Hague na ƙasar Netherlands wadda ke shari'ar waɗanda su ka aikata manyan laifi yaƙi ta ce ta samu tsohon shugaban Liberia Charles Taylor da laifin tallafawa 'yan tawaye ƙasar Saliyo aikata muggan laifuka yaƙi lokacin yaƙin basasar ƙasar. Ahmed Salisu ya bibiya zaman kotun ga kuma rahoton da ya haɗa mana.

Mai shari'a Richard Lussick kenan wanda ya jagoranci shari'ar ta Charles Taylor ya ke bayyana cewa an gurfanar da shi ne saboda zarginsa da ake yi kan laifukan yaƙi guda goma sha ɗaya da su ka haɗa da kisan kai da yi wa mata fyaɗe da sauran laifuka da su ka danganci musgunawa bani adama.

A zaman kotun dai wanda aka fara shi da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe agogon ƙasar Netherlands, alkalin ya ce bayan kammala shari'ar kotu ta samu wanda ake zargi da laifi.

Alkalin ya ce babu ko raba ɗaya biyu masu shari'a sun samu wanda ake zargi da samawa 'yan tawayen RUF da makamai da ma dai sojoji da tallafi iri-iri a yaƙin da aka yi a Saliyo.

A bisa wannan ne kotun ta ce ko shakka babu Charles Taylor ya kaimaka wajen hallaka mutane yayin yaƙin da aka yi a Saliyo anda ya yi sanadiyar hallaka mutane da dama da kuma rarraba mutane da matsugunanansu. To sai dai duk da cewar kotun ta samu shi tsohon shugban a Liberiya da laifi, a gefe guda kuma alkalin ya bayyana cewar hujjojin da aka gabatar a gaban kotun ba su gamsar da ita ba game da cewar shi ne ya yi uwa ya kuma yi makarɓiya wajen jagoranar yaƙin.

Dangane da wannan ne ya sa jagorar masu gabatar da ƙara Brenda Holis ta ce za su yi nazarin wannan batu tare da bayyana mastayinsu game da mastayin da kotun ta ɗauka. Jim kaɗan bayan kammala zaman kotun inda aka bayyana cewar an samu Mr. Taylo da laifi, mutane da dama a ƙasar Saliyo inda aka gudanar da yaƙin musamman ma dai wanda abin ya shafa su ka barke da sowa da ma dai kuka irin na farin ciki.

Nakasassu bayan shisshigin Taylor a SaliyoHoto: picture-alliance/dpa

Ya ce wanda ya barke da kukan murna bayan da alkali ya ce ya samu Charles Taylor da laifi inda ya ce mahaifiyata da mahaifi na su rasa rayaukansu yayin yakin. na yi asarar karatuna. Ina ganin alƙalin ya yi adalci ba wai hga Saliyo ba har ma da nahiyar Afrika baki ɗaya kuma wannan sako ne ga 'yan siyasa da shugabannin da ke tunanin za su musgunawa talakawa da ma dai aikata halin ɓera don kawai su azurta kansu.

Su ma dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bani adama daga ɓangagrori da dama na duniya sun nuna amincewarsu ga mastayin da kotun ta ɗauka inda su ka ce hakan zai zama 'yar manunuiya ga shugabanni masu irin wannan tunani. To sai dai yayin da mutane ke maraba da wannan mastayi da kotun ta ɗauka, lauyoyin da ke kare Mr. Taylor sun bayyana cewar ba su amince da hukuncin da kotun ta yanke ba kuma a su yi bakin ƙoƙarinsu wajen ganin sun ƙalubalanci duk irin hukuncin da za a yanke masa.

Ga alama ba lauyoyin Taylor ne kaɗai ke da ja da mastayin da kotun ta ɗauka ba, 'yan ƙasar shi Taylor ɗn ta haihuwa wato Liberiya ma sun nuna rashin amincewar inda su ce kotun ba ta yi adalci ba. Wani ɗan Liberiya kenan ya ke cewar dama mun san ba za su yi adalci ga jama'ar Liberiya ba a mastayin da za su ɗauka kan shari'ar. Amma dai su kwana da sani ba mu ɗauki wannan a masatyin wani ƙalubale ba, za kuma mu yi amfani da mataki na shari'a wajen ƙalubalantar matakin kotun. Baya ga haka ina jinjinawa 'yan Liberiya kuma ina son shaidawa Mr. Taylor cewar muna tare da shi, sai dai mutu ka raba.

Kotun hukunta masu laifukan yaki a birnin HagueHoto: AP

A halin da ake ciki dai, a ranar talatin ga watan gobe ne dai idan Allah ya kaimu kotu za ta bayyana irin hukunci da yankewa Charles Taylor wanda ke zaman tsohon shugaban ƙasa na farko da kotun ta yankewa hukunci kuma ana sa ran zai yi zaman kaso ne a Burtaniya kamar yadda aka amince tun bayan fara shari'ar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umru Aliyu