Cote d'Ivoire: Ouattara zai shiga takara
September 15, 2020Kotun kolin Cote d'Ivoire mai kula da harkokin zabe ta tabbatar da hudu daga cikin 'yan siyasar kasar da suka nuna sha'awarsu ta tsayawa takara, ko da ya ke kotun ta zayyana wasu muhimman dalilai da suka alkalai amincewa da takardun Pascal Affi N’Guessan na jam'iyyar (FPI), da Henri Konan Bédié tsohon shugaban kasar kuma kusa a kawancen jam'iyyun (PDCI), da kuma shugaba Alassane Ouattara na jam'iyyar (RHDP), kana da dankara guda mai zaman kansa da ake kira Kouadio Konan Bertin mai lakabi da KKB.
Tuni dai bangarori dabam-daban na kasar suka soma tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu, Joël N'guessan tsohon minista ne kuma kusa a jam'iyyar shugaban kasar Alassane Ouattara mai neman tazarce.
"Ya ce kotun tsarin mulki ta yi aiki tukuru domin kuwa ta bayyana hujjojin da suka sa suka yarda da wadannan mutanen da su tsaya takara, tare da bayyana dalilan da suka sa har 'yan takarar suka kasance mutun hudu kawai."
Wasu daga cikin manyan 'yan takarar da alkalan kotun suka yi watsi da takararsu sun hada da tshohon shugaban kasar Laurent Gbagbo, da tsohon firaminista kuma tsohon shugaban majalisar dokokin Cote d'ivoire Guillaume Soro, baya ga wasu tsoffin jiga-jigan gwamnatin kasar irinsu Mamadou Koulibaly, da Marcel Amon Tanoh wani tsohon na hannun daman Alassane Ouattara da suka raba gari. 'Yan adawa kasar dai sun yi mamakin ganin yadda kotun ta aminta da wannan tsarin kamar yadda Marie Noëlle Oullé ta jam'iyyar PDCI – RDA ke cewa.
"Ta ce sam sam bamu aminta da wannan tsari ba, kotu ta amince da takarar Alassane Ouattara domin baya da burin sake tsayawa takara a wani wa'adin mulki na uku hakan ya sabawa kundin tsarin mulki, kana kuma kotun ta kasance mai hannu dumu-dumu da taka kundin tsarin mulki."
A na shi bangare shima tsohon shugabnan majalisar dokokin kasar da yake mayar da martani kan matakin kotun, Guillaume Soro ya bayyana mamakinsa kan yadda alkalan kotun suka dauki wannan mataki.
A yanzu dai kama daga babban birnin kasar har ya zuwa babban birnin kasuwancin kasar da aka sha fuskantar tarzoma da zanga-zangar kin jinin wani karin wa'adin mulki na shugaba Alassane Ouattara ba abinda ke faruwa a yanzu inda daukacin manyan biranen aka jijjibge jami'an tsaro a cikin wani yanayi na shirin ko takwana.