Kotun Iran ta janye hukuncin kisa da aka yanke wa mawaki
June 22, 2024![](https://static.dw.com/image/68930277_800.webp)
Kotun kolin Iran ta janye hukuncin kisan da aka yanke wa fitaccen mawakin kasar Toomaj Salehi, wanda aka daure bayan samunsa da laifin tunzura jama'a gudanar da zanga-zanga sakamakon mutuwar matashiya Mahsa Amini a hannun jami'an tsaron kasar.
Karin bayani:Iran: Shekara guda da mutuwar Jina Amini
Lauyansa Amir Raisian ne ya wallafa janye hukuncin a shafinsa na X, yana mai cewa kotun kolin ta bada umarnin sake nazartar shari'ar, sakamakon kurakuran da ta ce an tafka a shari'ar, bayan tun da farko an yanke masa hukuncin kisan a cikin watan Afirilun da ya gabata.
Karin bayani:Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mutum uku
An dai kama mawakin mai shekaru 33 a cikin watan Oktoban shekarar 2022, bayan kazamar zanga-zangar da ta biyo bayan mutuwar matashiyar, wadda aka kama bisa laifin rashin yin lullubi.
Zanga-zangar dai ta janyo mutuwar darurun Iraniyawa ciki har da 'yan sanda.