Kotun kolin Jamus na nazarin karar haramta NPD ta 'yan Nazi
March 1, 2016Kotun tsarin mulkin Jamus ta dukufa kan karar da majalisar amintanttu ko dattawa ta shigar gabanta, ta neman a haramta jam'iyyar NPD ta 'yan Nazi, matakain da wasu ke ganin cewar ba zai magance matsalar kyamar baki da ake fuskanta a kasar ba. Kwanaki uku wannan kotu da ke da mazauninta a birnin Karlsruhe za ta shafe ta na zama don sauran bahasi daga bangarori daban daban.
Sai dai kotun tsarin mulki za ta dauki watanni kafin ta yanke hukunci a kan karar da aka shigar gabanta. Ita dai majalisar amintattu ko dattawa ta Jamus wato Bundesrat ta nunar da cewar manufofi da halayyar da jam'iyyar NPD ke nunawa sun saba wa kundin tsarin Mulkin Jamus.
Amma kuma shugaban Jam'iyyar NPD Frank Franz ya nesanta jam'yyarsa daga zargin da ake yi mata. ya ce "Idan aka duba halin da ake ci a fannin siysa , za a ga cewar duk sukar da jam'iyyar NPD ke yi na da ma'ana, domin duk abuwuan da ta yi ta gargadi a kai shekara da shekaru, su ne ke faruwa a fagen siyasa yanzu haka. ."