Kotun kolin Mali ta daure tsohon firaminista Choguel Maïga
August 19, 2025
Kotun kolin Mali ta daure tsohon firaministan kasar Choguel Maïga a wannan Talata, bayan zarginsa da aikata rashawa, wanda ya musanta aikata laifin.
Lauyansa mai suna Cheick Oumar Konaré, ya shaida wa manema labarai cewa an tsare wanda yake wakilta, kamar yadda babban mai gabatar da kara na kasar ya nema, bayan fitowar rahoton babban mai binciken kudi na kasar, wanda ya zargi Choguel Maïga mai shekaru 67 da aiakata badakala a lokacin da yake kan karagar mulki.
Mr Maïga ya rike firaministan Mali daga ranar 6 Yunin 2021, zuwa 20 ga Nuwamban 2024, inda da sojojin da ke mulki a kasar suka kore shi, bayan da ya soki lamarinsu kan dage zaben da zai mika mulki ga farar hula.
Daga nan ne ya ci gaba da caccakar manufofin gwamnatin Janar Assimi Goïta a fili, lamarin da ya fusata mahukuntan.
Karin bayani:Mali: Shekaru biyar bayan juyin mulki
Ko a farkon wannan wata na Agusta, hukumomin Mali sun cafke tsohon firaminista Moussa Mara, bayan jawabin da ya wallafa shafinsa na X da ke nuna goyon baya ga masu sukar gwamnati da ke daure a kurkuku, wadda ke mulki tun shekarar 2020 bayan juyin mulki.