1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotun kolin ta tabbatar da zaben gwamnan Kano

January 12, 2024

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da zaben gwamnonin jihohin Lagos, Bauchi, Kano, Zamfara, Plateau da Ebonyi a wani shri'a da ya dauki ahnkali a ciki da wajen kasar, matakin da tuni ya haifae da martani.

Nigeria Neuer Gouverneur von Kano
Hoto: Kyusufabba/Twitter

Ra'ayi dai yazo iri guda tsakanin daukaci na alkalan kotun guda biyar cewar kuskure ne babba, kwashe kuri'u 165,616 da kotunan baya su kai. Cikin wani hukuncin da ya dauki tsawon kusan sa'o'i biyu, kotun a karakshin mai shari'a John Okoro ta tabbatar da zaben Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano. Tun farko jihar Kanondai ta dau zafi a cikin faduwar gaba da ma tunanin rikici. To sai dai kuma sabon gwamnan Abba Kabir ya ce zafin na zaman na murna, ba wai tayar da hankalin mutane ba.

Karin Bayani: Kotun koli ta gama sauraron shari'ar Kano

Babu dai wakilan jam‘iyyar APC a cikin zauren kotun a wani abin da ke zaman alamun ilimin lamarin da ke tafe tun ma kafin ranar ta hukunci. To sai dai kuma ko bayan jihar Kano kotun ta kuma tabbatar da zaben gwamnonin Lagos, Bauchi, Zamfara, Plateau da Ebonyi.

Bala Abdulkadir Mohammed na zaman gwamnan jihar Bauchi da kuma ya ce a shirye yake ya rungumi daukaci na masu adawa a jihar. Sabbabin hukuncin dai ya kawo karshen gwagwarmaya mai zafi ta siyasa da ta dauki hankali ciki da ma wajen kasar.