Kotun Masar ta daure tsohon shugaba Morsi
April 21, 2015Talla
Wata kotun kasar Masar ta daure hambararren Shugaban kasar Mohamed Mursi na tsawon shekaru 20 a gidan fursuna, saboda musguna wa masu zanga-zanga amma an wankeshi daga laifukan da zai fuskanci hukuncin kisa.
A shari'a na farko kan tuhume-tuhumen da yake fuskanta kotun ta samu Mursi da laifin ba da umurnin cin zarafin masu zanga-zanga.
Mohamed Mursi ya zaben zaben demokaradiyya na farko a kasar ta Masar wanda ya gudana a watan Mayu na shekara ta 2012, amma gwamnatinsa ta kawo karshe a tsakiyar shekara ta 2013, bisa rarrabuwa da aka samu tsakanin al'umar kasar.