1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Masar ta rusa Majalisar dokoki

Zainab MohammedJune 14, 2012

Hukuncin kotun kolin Masar ɗin dai tamkar mayar da hannun agogo baya ne ga ƙungiyar 'yan uwa musulmi dake da rinjaye a majalisar, kuma ke bukatar soke takarar Ahmed Shafiq

Egyptian Opposition lawmakers protest inside Egypt's parliament after parliament late Monday March 19, 2007 approved a controversial set of amendments to the constitution that the opposition has denounced as a blow to democracy in this top U.S. ally in the Mideast. (AP Photo/Hossam Ali)
Hoto: dapd

Babbar kotun ƙasar Masar ta bada umurnin rusa majalisar dokokin ƙasar dake da rinjayen wakilan ƙungiyar 'yan uwa musulmi, tare da yanke hukuncin dake bawa tsohon priministan Hosni Mubarak, 'yancin takara a zagaye na biyun zaɓen shugaban ƙasa. Wannan dai tamkar duka biyu ne aka yiwa 'yan uwa musulmin, wanda kuma ka iya janyo dusashewar tauraronta a fagen siyasa, watanni 16 bayan nasarara hanɓarar da gwamnatin Hosni Mubarak. Wannan hukunci da kotun kolin tsarin mulkin masar ɗin ta yanke, wanda duk Alkalanta Mubarak ne ya naɗa dai, ya daɗa tsananta gwagwarmayar madafan iko tsakanin kungiyar ta 'yan uwa musulmi da sojojin dake mulkin kasar tun bayan kifar da gwamnatin Mubarak. Zartarwar kotun dai ya dada karfafa matsayin majalisar sojin, wanda kuma tamkar kwace ikon 'yan uwa musulmi dake da rinjaye a majalisar dokokin ƙasar ne, tare da karfafa gwiwar Ahmed Shafiq dake zama tsohon priministan Mubarak, kuma mutumin da keda goyon bayan majalisar mulkin sojin. Shugaban kungiyar 'yan uwa musulmi Mohammed el-Beltagy, ya bayyana hukuncin kotun da kasancewa cikkaken juyin mulki ne. A yanzu haka dai ƙungiyar ta 'yan uwa musulmi da sauran jam'iyyu masu sassaucin ra'ayi na kira da a gudanar da bore na ƙasa baki ɗaya.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu