1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotun MDD zata fara shari'ar Pretoria da Isra'ila kan Gaza

Zainab Mohammed Abubakar
January 11, 2024

A wannan Alhamis ne babbar kotun MDD ke bude zaman shari'ar da Afrika ta Kudu ta shigar na cewa, yakin da Isra’ila ke yi da kungiyar Hamas na kisan kiyashi ne kan Falasdinawa, ikirarin da Isra’ila ta musanta.

Hoto: International Court of Justice/UN Photo/Wiebe Kiestra

Da farko Afirka ta Kudu ta bukaci kotun kasa da kasarda ta bayar da umarnin dakatar da farmakin da sojojin Isra'ila ke kai wa a zirin Gaza cikin gaggawa, a matsayin wani bangare na shari'ar da ake ganin za a dauki tsawon shekaru ana yi.

Rikicin dai ya ta'allaka ne da kallon Isra'ila a matsayin kasar yahudawa da aka kafa bayan kisan kare dangi na Nazi. Hakanan kuma ya shafi asalin Afirka ta Kudu.

Jam'iyyar da ke mulki ta ANC ta dade tana kwatanta manufofin Isra'ila a Gazada Yammacin Kogin Jordan da tarihinta a karkashin mulkin wariyar launin fata na 'yan tsirarun fararen fata, wanda ya takaita 'yancin yawancin bakar fatar kasar kafin ya kare a shekarar 1994.