1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotun Nijar ta cire rigar kariyar Mohamed Bazoum

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 14, 2024

Bazoum din zai fuskanci zargin daukar nauyin ayyukan ta'addanci da cin amanar kasa

Hoto: Stevens Tomas/ABACA/IMAGO

Kotun Jamhuriyar Nijar ta cire rigar kariyar hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum, domin bada damar tuhumarsa a gaban shari'a, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi masa a cikin watan Yulin bara.

Karin bayani:An sauya lokacin shari'ar Bazoum

Shugaban kotun, wadda aka kaddamar a cikin watan Nuwamban bara Abdou 'Dan Galadima ne ya sanar da janye kariyar, inda Bazoum din zai fuskanci zargin daukar nauyin ayyukan ta'addanci da cin amanar kasa, kamar yadda sojojin da ke mulki suka nuna, bayan wayar tarho da ya yi da shugaban Faransa Emmanuel Macron da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, wadanda suka yi tayin amfani da karfin soji don tallafa masa.

Karin bayani:Nijar: Ana shirin cire rigar kariyar Bazoum

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil'adama ciki har da Human Rights Watch suka soki wannan mataki, tare da sanya ayar tambaya kan hurumi da kuma sahihancin kotun, inda suka ce idan har ana zargin Bazoum da wani laifi to kamata ya yi a gurfanar da shi a gaban cikakkiyar kotu, tare da yi masa adalci wajen saurare.