1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Kotun Pakistan ta daure tsohon firaminista Khan da matarsa

Mouhamadou Awal Balarabe
January 17, 2025

Alkali Nasir Javed Rana ya samu Imran Khan da laifin cin hanci da rashawa da amfani da mukaminsa na firayiminista ba bisa ka'ida ba, yayin da ya samu mai dakinsa da laifin taimakawa wajen aikata laifi .

Tsohon Firaminista Imran Khan da matarsa Bushra Bibi
Tsohon Firaminista Imran Khan da matarsa Bushra Bibi Hoto: K.M. Chaudary/AP Photo/picture alliance

Wata kotu a Pakistan ta yanke wa tsohon Firaminista Imran Khan hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari, bisa samunsa da laifin cin hanci da rashawa da ke da alaka da binciken badakalar kudi da aka gudanar. Alkali Nasir Javed Rana ne ya yanke hukuncin a wata kotun da aka kafa a cikin gidan yarin da Khan ke tsare, inda ya same shi da wani karin laifi na amfani da mukaminsa na firayiminista ba bisa ka'ida ba.

karin bayani: An haramta wa Imran Khan rike mukami a Pakistan

Sannan mai shigar da kara Muzaffar Abbasi ya shaida wa manema labarai cewar an yanke wa mai dakin Khan, wacce ita ma  ake tuhuma a shari'ar, hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari saboda ta taimaka wajen aikata laifi. Sai dai lauyansa Faisal Chaudhry ya ce  jam'iyyar Imran Khan na da niyyar kalubalantar hukuncin a kotu na gaba, saboda taba alakanta hukunci da bita da kullin siyasa.