Kotun sauraron ƙarar maguɗin zaɓe ta soke zaɓen gwamnan jihar Kebbi
October 20, 2007Talla
Kotun sauraron kararrakin magudin zabe a jihar Kebbi ta tarayyar Nijeriya ta yanke hukuncin cewa gwamnan Saidu Usman Dakin Gari yanzu ba shi ne gwamnan jihar ba dole sai an sake zabe. Mai shari´a Andrew Kaka shi ne ya yanke wannan hukunci bayan ya kafa hujjoji wadanda suka hada da cewar a lokacin da aka gudanar da zabe, gwamna Saidu Usman Dakin Gari ba cikakken dan jam´iyar PDP ba ne kuma a lokacin da ya canza sheka daga ANPP zuwa PDP babu cikakkun takardun da ke tabbatar da cewa ya bar jam´iyar ta ANPP. Kotun ta ba shi damar daukaka kara na wannan hukunci da ta yanke a yau.