1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun tsarin mulki a ƙasar Masar ta rusa majalisar dokoki

June 15, 2012

Taƙaitacen tarihin yan takarar zaɓen ƙasar guda biyu wato Ahmed Chafik da Mohammed Mursi

epa03264238 Egyptian protesters and security forces are seen outside the Supreme Constitutional Court, in Cairo, Egypt, 14 June 2012. The court on 14 June will review the legality of a law barring senior officials from the regime of deposed president Hosni Mubarak from running for public office. If it upholds the ban, that could see Ahmed Shafik, Mubarak's last premier, barred from standing in this weekend's race, and the possible cancellation of the election - throwing the country's democratic transition into confusion. EPA/KHALED ELFIQI +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Mohamed Mursi dan shekaru 60 da haifuwa kana kuma cikakken injiniya wanda ya yi karatunsa a Amurka, takarar da sunnan jam'iyyar yan uwa musulumi ta zoma sa ne ba zato ba tsamani. Bayan da kotun ta haramta wa ɗan takara na farko da jam'iyar ta gabatar mata wato Khairate Al Chater wanda aka soke takarar sa saboda wasu dalilai kan cewar an sha kuleshi a gidan kurku a lokacion mulkin Hosni Mubarak:

Mohamed wanda ya kasance shugaban gungun jam'iyar yan uwa musulmi a majalisar masar kafin daga baya a rusa jam'iyar ya ƙwashe kusan tsawon rayuwar sa ya na gwaggwarmaya a cikinta. A shekara ta 2006 bayan ya dawo da Amurka gwamnatin Hosni Mubarak ta kuleshi a gidan kurku sakamakon wani yamutsin da ya auku wanda kuma ake da zaton cewa ya na daga cikin waɗanda suka kitsa shi.

ba tabas Mursi ya samu nasara a zaɓen

Mohammed Mursi da Ahmed SchafikHoto: picture-alliance/dpa

Haka dai ya yi tsa gwagwarmayar har zuwa shekara ta 2011 lokacin da jam'iyar ta yan uwa musulmi ta rikiɗe zuwa jam'iyar PLJ le parti pour la liberte et la justice wanda kuma jam'iyar ta zaɓe shi a matsayin jagora.Tun bayan juyin juya halin da ya kifar da gwamnatin Hosni Mubarak da aka ƙudirir aniyar shirya zaɓe ,jama'a na ganin jam'iyar yan uwa musulmin za ta iya taka muhimiyar rawa kuma tun can da farko shi kan sa Mohamed Mursi bai yi tsamani shi ne zai yi takarar ba domin an riga a ƙaddamar da mataimakin sa ,sai dai kuma rabo ya yi halinsa.

Hammdi El Aouni wani ƙwarara ne kan ƙasar Masar da ke a jami'ar birnin Berlin na nan Jamus wanda a cikin wata hira da DW ta yi da shi ya sheda cewar ''ya ce Mohammed Mursi mutin ne kamuli nutsatse wanda ke da manufofi na tattaunawa a kullum ,sai dai ya ce har yanzu ya na nan akan hakidarsa ta musulumci.Masu lura da al'amura na ganin cewar ɗan takarar da zai ƙalubalanci Morsi ɗin Ahmed Chafik mai shekaru 70 a duniya tsohon kwamanda mayakan sama na iya samu mulkin cikin sauƙi saboda ga alama yana da goyon baya sojoji. Tsohon ministan sufirin jiragen sama wanda kuma shi ne ya jagoranci sayar da hanayen jarin kamfanin sufirin jiragen sama na ƙasar ya na da amana da yarda ta masu saka jari na ƙasashen duniya.

Fargaban sake komawa mulkin kama kariya tare da Chafik

Bayan karatunsa na aikin mayaƙan sama na soji Chafik ya kasance matuƙin jiragen yaƙi ,a shekara ta 1973 an baiyana shi a matsayin jarumi kana gwarzo bayan yain Kippour sannan a shekarun 1980 ya kasance wakilin soja a ofishin jakadancin Masar a Rome sannan tun shekara ta 1990 shi ne shugaban hafsan hafsoshosin mayaƙan sama na Masar har zuwa shekara ta 2002.Kana ya na daga cikin tshofin manbobin gwamnatin Muarak da guguwar dimokaradiyar da ta biyo bata biya da su.Sai dai ya shiga garari a lokacin da tsohon shugaban ya miƙasa matsayin framinista a ranar 29 ga watan janeru na shekara ta 201 1 a tsakiyar boran juyin juya hali da aka yi domin ƙwantar da tarzomar masu zanga zanga amma ba shiri ya salama ga matsayin saboda matsin lambar masu zanga zanga.

Masu bore a birnin AlƙahiraHoto: Reuters

Wani abin da ake ganinsa da shi mai kyau shi ne cewar Chafik na daga cikin tshofin jami'an tsohuwar gwamnatin wanda ba a same shi da laifin sota ba.Mista Hammdi ya ce Ahmed Chafik ɗin mutun ne mai ra'ayin ci gaba da faɗaɗa hulɗa to amma ya baiyana cewar ''yan ƙasar ta Masar na da fargaban kada ya samu mulkin ya sake dawo da mulkin kama kariya irin na wacan lokaci abinda ka iya zama babban koma baya a irin gwagwarmayar da jama'ar ƙasar su ka yi.A yanzu dai da kotun tsarin mulki ta halartar da takara sa ana hasashen cewar ba ma kawa ya na kan hanyar samun nasara a zaɓen ta kwane hali idan har al'ummar kasar basu tada bali ba na haramta zaɓen.

Daga ƙasa za a iya sauraron sautin wannan rahoto

Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar