1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Kotun Thailand ta haramta babbar jam'yyar adawa

Suleiman Babayo ATB
August 7, 2024

Kotun tsarin mulkin kasar Thailand ta rusa babbar jam'yya mafi girma na yawan 'yan majalisar dokoki bayan kwashe tsawon lokaci ana kai ruwa rana na siyasa.

Thailand | Pita Limjaroenrat
Pita Limjaroenrat shugaban jam'iyyar Move Forward Party da aka rusa a kasar ThailandHoto: Chatkla SamnaingjamAP Photo/picture alliance

Babbar kotun kasar Thailand ta yanke hukuncin rusa babbar jam'iyyar adawa ta kasar ta Move Forward Party, shekara guda bayan masu ra'ayin gaba-dai gaba-dai da suka kafa jam'iyyar sun samu nasarar lashe mafi yawan kujerun majalisar dokokin kasar fiye da kowace jam'iyya amma sun gaza samun nasarar iya kafa gwamnati, a kasar da ke yankin kudu maso gabashin Asiya.

Kotun tsarin mulki da ke birnin Bangkok fadar gwamnatin kasar ta yanke wannan hukunci na haramta jam'iyyar da Pita Limjaroenrat yake jagoranta, wanda shi kansa dan siyasar mai farin jini an yanke masa hukuncin hana shiga harkokin siyasa na shekaru 10.

Ita dai jam'iyyar adawar da aka haramta da musanta zargin da ake mata na raina masarautar kasar ta Thailand mai karfin fada aji.