SiyasaAfirka
An bayar da belin Bobi Wine a Yuganda
November 20, 2020Talla
Kamun da aka yi magudun adawa Bobi Wine a ranar Laraba ya haifar da zanga-zanaga wace kawo safiyar Jumma'ar nan ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 38.
Robert Kyagulanyi wanda ake yi wa lakabi da Bobi Wine ya yi fice a fagen waka a Yuganda kuma daga bisani ya rikide ya koma dan siyasa har ma a yanzu ya zamarwa Shugaba Yoweri Mosevni babban mai adawa a zaben watan Janairu mai zuwa. An kama shi ne bisa laifin karya dokokin corona ta hanyar shirya gangamin yakin neman zaben da ya tara fiye da adadin mutanen da hukumomi suka kayyade.
Sai dai kuma matasa na ci gaba da yin adawa da lamarin ta hanyar zanga-zanga.