1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koyar da 'yan mata kyauta

June 7, 2017

Wani matashin Malamin jami'a yana koyar da makarantar 'yan mata kyauta domin kyautata harkokin ilimi a Jihar Katsina da ke Najeriya.

UNICEF Bilder nur für Sabina Casagrande
Hoto: UNICEF/GIACOMO PIROZZI

A Jihar Katsina da ke Najeriya wani matashin malami a Jami'ar Umaru Musa Yar'adua da ke Katsina ya sadaukar da kansa wajen zuwa ya koyarwa a wata makarantar sakanderen mata kyauta. Wannan matashi dai kullun ya kan samu awa biyu zuwa uku ya je makarantar ya koyar idan ya kammala darusan da yake dauka a jami'a.

Wannan matashi Malami dai Dr Musa Ahmed Jibril Mashi ya yi aniyar ba da irin wannan taimakon ne bisa la'akari da taimakon da ya samu a lokacin da yake gudanar karatu. Wannan fasahar ta zo lokacin digiri na uku a kasar Afirka ta Kudu a shekara ta 2015 sai ya tsaya ya yi nazarin cewa a rayuwa tun da yake karatu bai taba kashe sama da naira dubu biyar ba to ganin cewa kudin Talakawa aka dauka aka biya masa kudin karatu shi ya sa yake haka.

Amma sai dai Dr Jibril ya koka kan irin ci baya da ake samu a Jihar Katsina wajen harkar ci gaba ilmin wanda ke kara kara masa gwarin gwiwar koyarwa kyauta a makarantar mata.