1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kremlin ta amince da tsagaita bude wuta a Ukraine

Binta Aliyu Zurmi
January 31, 2026

Fadar mulki ta Kremlin ta tabbatar da cewa Shugaba Donald Trump ya bukaci Shugaba Vladimir Putin da ya dakatar da hare-haren da ake kai wa birane da garuruwan Ukraine na tsawon mako guda.

Russland Moskau 2025 | Wladimir Putin hält Neujahrsansprache an die Nation
Hoto: Mikhail Metzel/Sputnik/REUTERS

Sai dai Kremlin ta ce duk da Rasha ta amince da wannan bukata, amma za ta dakatar da kai hare-harenta ta sama a Kyiv har zuwa ranar 1 ga Fabrairu ne kawai. 

Tun da farko shugaban kasar Volodymyr Zelenskyy ya ce Ukraine za ta daina kai hare-hare kan Rasha idan Rasha ta dakatar da kai hare-hare kan kayayyakin makamashin Ukraine.

Zelensky ya ce shawarar tsagaita bude wuta ta fito ne daga Washington.

Shugaban Ukraine ya kuma ce masu shiga tsakani sun kasa cimma matsaya kan iko da yankin Donetsk dake gabashin Ukraine. Wanda Rasha ke neman Ukraine ta mika yankin da ya jima karkashin ikon ta.

Ana sa ran ci gaba da tattaunawa atsakanin bangarorin biyu da kuma masu shiga tsakani a birnin Abu Dhabi na kasar hadaddiyar Daular Larabawa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW