Kuba ta samu sabon shugaban kasa
April 19, 2018Talla
A jawabinsa na farko a matsayinsa na shugaban kasar ta Kuba, Miguel Diaz-Canel, ya ce al'ummar kasar Cuba ta damka masa jagorancin kasar domin ya dasa daga inda aka taya a wannan lokaci mai cike da tarihi da kasar ke fuskantar sauye-sauye inda ya ke cewa "na dauki nauyin da ya rataya a kaina na wanda aka zaba tare da tabbacin cewa dukannin masu ra'ayin juyin-juya hali na kasar Kuba ko ma wane mukami muke da shi, ko ma wane aiki muke yi."
'Yan majalisar dokokin kasar ta Kuba ne dai suka zabi Miguel Diaz-Canel a matsayin sabon shugaban kasar na tsawon shekaru biyar wanda ake iya sabuntawa bayan kawo karshen wa'adin mulki na biyu na Shugaba Raul Castro Ruz.