1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kudancin Sudan ta zama mambar MƊD

July 14, 2011

Kudancin Sudan ta sami kyakkyawar tarba a matsayin wakiliya ta 193 a cikin MƊD

Ban Ki-Moon (dama) tare da mataimakin shugaban kudancin Sudan Riek Machar Teny-Dhurgon a New York(13.07.11)Hoto: picture alliance/dpa

Babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da jamhuriyyar kudancin Sudan a matsayin ƙasa ta 193 dake da wakilci a cikin majalisar, bayan da kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya yayi na'am da matakin a ranar Laraba (13.07.11). Shigar da sabuwar ƙasar ta zo ne kwanaki ƙalilan bayan da ƙasar ta ayyana samun 'yancinta biyo bayan tsawon shekaru 50 da ta yi tana gwabza yaƙin basasa tare da gwamnatin Sudan, wanda yayi sanadiyyar mutuwar miliyoyin jama'a. Duk da cewar kudancin Sudan tana ɗimbin albarkatun man fetur dake jibge, amma tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi talauci a duniya, abinda ya sa sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ko Moon ya ce ƙasar na buƙatar tallafi:

" Yace, jaririyar ƙasar Sudan da aka samar a yau(14.07.11) tana fama da koma baya a ɗaukacin abubuwan da suka shafi ci gaban rayuwar al'umma. Saboda haka, kamar kowace jaririyar ƙasa tana buƙatar taimako. Alhakin dake kanmu yana da yawa kuma rawar da Majalisar Ɗinkin Duniya za ta taka tana muhimmanci, amma kuma mai sarƙƙaƙiya."

Sai dai a jawabin nuna farin ciki ga zama mambar majalisar Ɗinkin Duniyar da mataimakin shugaban kudancin Sudan Riek Machar Teny-Dhurgon ya yi, ya ce a shirye suke su tinkari ƙalubalen dake gaban su :

" Jamhuriyyar kudancin Sudan za ta kasance mai sauke nauyin daya rataya a wuyanta a tsakanin al'ummomin ƙasashen duniya, kuma za ta yi abinda ya wajaba akanta a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa. Muna ɗaukar matakan cimma burin mutunta ɗaukacin yarjeniyoyin duniya musamman wadda ta shafi kare haƙƙin bil'Adama cikin hanzari."

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal