1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kudancin Sudan: ´yanci cikin uƙuba

June 2, 2011

A daidai lokacin da kudancin Sudan ke shirin bikin samun ´yanci al´ummomin yankin na fama da uƙubar rayuka

Salva Kiir shugaban yankin kudancin SudanHoto: AP

Ranar tara ga wata mai kamawa yankin kudancin Sudan zai bikin  samun yancin kai, to saidai yankin na fama da matsaloli masu tarin yawa mussaman ta fannin tsaro.

 A halin da ake ciki, dubunan al´ummomin birnin Abyei da kewaye sun ƙaura dalili da saban rikicin da ya ɓarke, sannan a ɗaya hannun, kudancin Sudan na fuskantar hare-hare daga ´yan tawayen LRA na ƙasar Uganda

Birnin Abyei dake kan iyaka tsakanin yankunan kudu da na arewacin Sudan ya shiga wani halin  na tsaka mai wuya tun bayan da sojojin  gwamnatin Khartum suka kai masa mamaya a watan da ya gabata.

Wasu alƙallumam Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi nuni da cewar fiye da mutane dubu 60 su ka shiga gudun hijira domin ƙauracewa tursasawar sojojin mamayar.

To saidai kuma bayan matsalar Abyei  suma dakarun tawaye na LRA na ƙasar Uganga suna na cigaba da gallazawa al´ummar kudancin Sudan da ke zaune a iyaka da Uganda. Charles matashi ne, wanda shi ganau ne ba jiyau ba, game da wannan mayuyacin hali da al´ummomin kudancin Sudan ke fama da shi:

"Sun ɗaure ni da igiya sannan sun ka yi min duka a lokacin da na yi yunkurin tserwa sai su ka sare ni da wata adda."

Fiye da shelkaru 20 da suka wuce ƙungiyar tawayen LRA bisa jagorancin Joseph Kony ke cin karenta babu babbaka a yankunan iyakokin  Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Jamhuriya Demokradiyar Kongo, Uganda da kudancin Sudan.

Charles wanda ya yi nasarar kubuta daga hannun tsagerun LRA, ya samu kulawa ta mussamman daga wata cibiyar bada horo dake birnin Yambio na kudancin Sudan, wanda ke samar da agaji da kuma magugunan ga matasan da su ka yi fama da uƙubar LRA.

Justin Ebere shine shugaban wannan cibiya, ya bayyana irin wulakancin da yaran suke gani daga LRA

"Idan su ka kama yaro su kan ilasta masa ya kashe mahaifinsa ko mahaifiyarsa, domin kar ma su samu tunanin sulalewa bayan sun shiga runduna LRA, sam suna fidda ma su shawar zama cikin jama´a."

Ya ce LRA na koyar da matasan ɗabi´o´i irin  na rashin imani da rashin tausayi.

Grace itama wata budurwa ce ta sami kanta cikin hanin yan tawayen LRA kusan shekara guda.Ta yi nasara samun kuɓuta a lokacin wani samame da sojojin Uganda su ka ƙaddamar.

Ma´aifiyarta Esther ta shaida halin rayuwar da ta ke ciki yanzu:

"Ta na cikin damuwa ƙwarai.Wani lokacin sai ta yi shuruuu ba gama.

A duk lokacin da ta shiga irin wannan yanayi ba ta buƙatar wani ya dame ta da tambaya mussamman  wadda ta shafi rayuwarta tare da  LRA".

Wannan hare-hare da LRA ke cigaba da kaiwa ayankin kudancin Sudan , ya sa har kullum mutane na shiga halin gudun hijira.

Mazauna garuruwa kamar su Sangua, da Nzara sun ce a halin yanzu  ba za su iya komawa cikin garuruwansu ba, saboda matsalar tsaro.

Idan aka yi la´akarin da rikicin Abyei da yanƙin cikin gida tsakanin mazauna kudancin Sudan a Malakal, sannan ga kuma matsalar ƙungiyar tawayen LRA, ko shakka babu, sabin hukumomin yankin kudancin Sudan da zai bikin yancin kai ranar tara ga wata mai kamawa na da jan  aiki  a gabansu.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohammad Nasiru Awal