Aski kan kula da lafiyar kwakwalwa a Kenya
July 8, 2026
A babban asibitin kula da masu larurar kwakwalwa na Mathari da ke Nairobi babban birnin kasar Kenya, ana amfani da wata hanya ta musamman wajen taimaka wa marasa lafiya domin farfadowa cikin sauri.
Baya ga magunguna da shawarwari daga kwararru, wasu masu aski biyu kan rika ziyartar asibitin domin yi wa marasa lafiya aski da gyaran fuska ba tare da karbar ko da sisin kwabo ba.
Matakin taimakon marasa lafiya
Ma'aikatan asibitin sun ce gyaran jiki da tsafta na daga cikin muhimman abubuwan da ke taimaka wa masu fama da matsalar kwakwalwa su dawo da kwarin gwiwa da ma mutuncinsu.
Daya daga cikin alamomin da ke nuna cewa mutum na fama da matsalar lafiyar kwakwalwa a cewar masana, shi ne daina kula da tsaftar jiki ko kuma rashin sha'awar gyaran kai. Saboda haka, aski da gyaran fuska na taimaka wa marasa lafiya su ji suna da daraja tare da kara musu kwarin gwiwar komawa rayuwa ta yau da kullum.
Alkaluman gwamnati sun nuna cewa kusan kashi 25 cikin dari na masu zuwa asibitocin waje a Kenya, da kuma kashi 40 cikin dari na wadanda ke kwance a asibitoci, suna fama da wata matsalar lafiyar kwakwalwa.
Jami'in jinya a asibitin na Mathari, Titus Enko ya ce mutane da dama kan fi mayar da hankali kan magunguna da shawarwari, su manta da muhimmancin tsaftar jiki alhali kuwa ba nan gizon ke saka ba.
Matsayin kwararru
Kwararrun masana sun ce damuwa mai tsanani da kuma matsananciyar fargaba na daga cikin matsalolin da aka fi gani, yayin da shaye-shayen miyagun kwayoyi ke ci gaba da zama babban kalubale, musamman a tsakanin maza.
A daidai lokacin da ake gudanar da watan wayar da kan jama'a kan lafiyar kwakwalwar maza, jami'an asibitin suna kira ga maza da su rika bayyana damuwarsu maimakon komawa ga shaye-shaye domin neman mafita.
Kungiyar Uniquely Gifted ce ke shirya wannan aikin gyaran jiki kowane wata. Wanda ta kafa kungiyar, Sheila Lugaliki, ta ce ita ma ta taba kwanciya a sashen masu fama da matsalar kwakwalwa, kuma abin da ta gani a lokacin ne ya sa ta kuduri aniyar komawa domin tallafa wa marasa lafiya.
Masana sun ce wannan ya nuna cewa kula da lafiyar kwakwalwa ba ta tsaya kan magani kadai ba, har ma tana bukatar hanyoyin da za su dawo wa mutum da mutunci, kwarin gwiwa da kuma jin cewa shi ma muhimmin bangare ne na al'umma.