1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kula da muhalli a Muzambik

Cristiane Vieira Teixeira/ Ahmed SalisuMay 18, 2016

Wata kungiya da ke kula da muhalli da yawon bude idanu ta dukufa wajen nunawa duniya cewar baya ga talauci kasar Muzambik na da arziki da kuma dumbin tarihi

AoM Mozambique Mafalala Tours
Hoto: DW

A kokarinsu na ganin sun sauya irin tunanin da baki ke da shi game da kasar Muzambik, wasu mutane na wata kungiya da ke da kula da muhalli da yawon bude idanu sun dukufa wajen nunawa duniya cewar baya ga talauci kasar na da arziki da kuma dumbin tarihi a sassa daban-daban ciki kuwa har da garin Mafalala da ke kusa da babban birnin kasar wato Maputo.

Wannan kungiyar Iverca Tourism and Environmental Association ta maida hankali ne wajen bada labarin yanayi da birnin Mafalala ke ciki musamman ma irin sauyin da aka fuskanta bayan da kasar ta Mozambik ta samu 'yancin kanta daga hannun turawan mulkin mallaka. 'Ya'yan kungiyar kan shirya ziyara ta gani da ido ga baki 'yan yawon bude idanu a cikin garin da ma bada labarin halin da ya ke ciki lokacin mulkin mallaka.


Ya ce "nuna wa al'umma irin banbance-banbancen da muke da su na da muhimmanci wajen sauya irin tunanin da suke da shi game da wannan garin da ma kasar da baki daya. Wannan abu ne da za a iya cewa ginshiki na kawo sauyi."

Baya ga yanayi na garin na Mafalala da kuma dimbin tarihin da ya kunsa, wasan kwallon kafa wani abu ne da za a iya cewar ya shara a yankin, kuma ya sanya shi yi suna matuka musamman ma a shekarun 1960 domin kuwa daya daga ciki shahararrun 'yan wasa na Portugal a garin na Mafalala ya girma, wannan ne ya sanya 'yan wannan kungiya ganin dacewar bayyanawa duniya wannan batu.

Siyasa ma dai na daga cikin batutuwa da wannan kungiya ta Iverca Tourism and Environmental Association ke maida hankai a kai domin a cewar jami'an kungiyar mutum biyu da suka shugabanci kasar sun fito daga Mafalala ne wanda ba kowa ne ya san da haka ba shi ne ma ya sanya suka ga dacewar shidawa duniya.