1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar ADF ta kashe mutane 31 a Kwango

July 28, 2026

Akalla fararen hula 31 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da ake zargin mayakan kungiyar ADF sun kai a lardin Ituri da ke arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.

Shugaban Kwango Felix Tshisekedi
Shugaban Kwango Felix TshisekediHoto: Fabrice Coffrini/AFP

Rahotanni sun ce hare-haren sun faru tsakanin ranar Larabar makon da ya gabata zuwa ranar Litinin, inda akalla mutum 18 suka mutu a kauyen Njiapanda-Bela da ya yi fice wajen ma'adinai. Sai dai wasu majiyoyin tsaro sun ce adadin wadanda aka kashe na iya kaiwa kusan 50.

Karin bayani :  Kungiyar ADF ta kashe mutane 31 a Kwango

Kungiyar ADF mai alaka da kungiyar IS na ci gaba da addabar yankunan Ituri da Arewacin Kivu, inda ake zarginta da kashe fararen hula da kuma karbar haraji daga manoma da masu hakar ma'adinai.Harin ADF mai alaka da IS ya kashe mutane kusan 40 a KwangoHarin ta'addanci ya kashe mutanen Jamhuriyar Kwango kusan 20

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani
Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW