1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar AES ta soke kudin Roaming na kiran waya

Salissou Boukari
November 22, 2024

A mataki na karfafa dangantaka da kawo sauki tsakanin al'umomi na kasashen AES, da suka hada da Nijar da MaliI da Burkina Faso, hukumomin kasashen uku sun rattaba hannu kan soke kudin kiran waya na roaming

Wata yar kasuwa na kiran waya don bunkasa kasuwanci
Wata yar kasuwa na kiran waya don bunkasa kasuwanciHoto: P. U. Ekpei/AFP/Getty Images

Kungiyar kawancen kasashen yankin Sahel AES da ta hada da Nijar da Mali da Burkina Faso, ta rattaba hannu kan yarjejeniyar saukaka sadarwa tsakanin kasashen. A baya dai Ministocin sadarwa na kasashen uku sun dauki wannan mataki ne a kokarin kawo sauki a fannoni daban-daban ga al'umominsu kuma da yake Magana ministan sadarwa na kasar Mali ya ce matakin babban ci gaba ne 

"Lamarin zai kawo sauki a fannin sadarwa domin idan ka dauki wayarka ta hannu daga Nijar zuwa Burkina ko Mali ko daga wadannan kasashe zuwa Nijar babu wani sauyi domin ba za a cire maka kudade na kiran da ka yi a wata kasa ba. Sauki ne ga al'umma musamman masu bulaguro domin”

Wani matashi dauke da wayar salulaHoto: Donwilson Odhiambo/Zuma/IMAGO

Daga nasu bangare ma'aikatan kamfanin sadarwa na kasar Nijar wato Niger Telecom sun jinjina wa kasashen uku dangane da daukar wannan mataki, inda a cewar shugaban gamayyar kungiyoyin Kwadago na Nijar Telecom Maman Lawali Moussa, babbar dama ce ga al'umomin kasashen uku

Matakin dai na a matsayin dage shinge a fannin sadarwa a tsakanin wadannan kasashe guda uku wanda ala tilas kasashen suka soke wasu kudade da ake samu don ganin al'umma ta samu saukin rayuwa.

Wasu matasana duba wayoyinsu na hannu Hoto: AFP/S. Heunis

A hannu daya, ita ma kasar Togo ta hanyar shugaban hukumar da ke sa ido kan kamfanonin sadarwa na kasar da ya halarci taron rattaba hannu kan wannan yarejejniya a birnin Yamai, ya ce abin da yake fata shi ne ganin an kai ga cimma irin wannan yarjejeniya tsakanin kasarsa Togo da Nijar da Burkina Faso, inda yace tuni suna da wannan yarjejeniya tsakaninsu da Mali, kuma wannan mataki ke daga cikin matakai da kasashen ke dauka na cire duk wani tarnaki da zai takura wa al'umomin kasashen uku a fannin zirga-zirga da karfafa huldar kasuwanci ta zamantakewa.