'yan gudun hijira za su rabauta da sana'oi a Najeriya
September 12, 2019Mista Maurer ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da masu masana'antu da 'yan kasuwa a jihar Lagos da ke tarayyar Najeriya a wannan rana ta Alhamis.
Yankunan da kungiyar ta zaba don fara gwajin wannan al'amari sun hada da jihohin da rikici ya raba al'umma d muhallansu da sansanin 'yan gudun hijira da kuma 'yan cirani.
Shugaban ya bayyana cewar sun gudanar da aikin samar da ruwan sha don samun riba a Arewa maso Gabashin Najeriya da kuma rabon wata na'urar binciken cututtuka a tsakanin kananan yara a Sudan ta Kudu, ayyukan da suka taimaki al'ummar yankunan da kudaden shiga da kuma abin yi.
Daga cikin 'yan kasuwar da suka halarci taron na Legas akwai Tony Elumelu guda cikin attajiran Najeriyar wanda ya yabawa wannan yunkuri na kungiyar agajin tare da jan hankalin kamfanoni su dubi wannan shiri a matsayin hanyar juya kudade.