Kungiyar Al-Shabaab ta nada sabon shugaba
September 6, 2014Talla
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito wata kafa da ke sanya idanu kan kungiyoyin 'yan tarzoma mai suna SITE na cewar kungiyar ta nada Sheikh Abu Ubaida Ahmad Umar don ya cigaba da jan ragamar kungiyar.
A sanarwar ta kuma ce ta kuma ce Al- Shabaab din za ta cigaba da biyayya dari bisa dari ga kungiyar Al-Qaida. Sheikh Abii Ubaida Ahmad Umar dai zai maye gurbin tsohon shugaban kungiyar Ahmad Abdi Godane ne wanda ya rasu sakamakon wani harin jiragen yakin Amirka da ya rutsa da shi a farkon mako.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman