1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Al-shabab na cigaba da zama barazana ga tsaro a Mogadishu

October 8, 2011

Dakarun Ƙungiyar Tarayyar Afirka da na gwamnatin Somaliya sun kai hari a wasu yankunan Mogadishu domin tasa ƙeyar 'yan ƙungiyar al-Shabab

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar AfirkaHoto: AP

Dakarun Ƙungiyar Tarayyar Afirka da na gwamnatin Somaliya sun ƙaddamar da hare-hare a ɗaya daga cikin gundumomin Mogadishu domin tasa ƙeyar duk wani ɗan ƙungiyar al-Shabab da ya rage a yankin. A wani yunƙurin da ke zuwa watanni biyu bayan da ƙungiyar ta ficce daga birnin. Wannan hari ya yi mafari ne bayan da ƙungiyar wacce ke da dangantaka da ƙungiyar Al- Ƙa'ida ta kai wani mummunar harin da aka daɗe ba'a gani ba tun bayan tsagaitawar yaƙin, lokacin da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da wasu bama-bamai a cikin wata mota a harabar wani ofishin gwamnati, wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 82. Kwamandan dakarun Ƙungiyar Tarayyar Afirka, Maj. Gen. Fred Mugisha ya faɗa wa kamfanin dillancin labarun Faransa wato AFP cewa dakarunsa sun karɓi jagoranci kusan kashi 95 na birnin Mogadishun tun bayan ficcewar 'yan tawayen. Duk da cewa ƙungiyar ta fice daga Mogadishu inda ta mamaye na kusan shekaru 4 tana cigaba da zama babban barazana ga tsaro.

Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Halima Balaraba Abbas