1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

AU: Rigakafin AstraZeneca na da inganci

March 18, 2021

Kungiyar Tarayyar Afirka ta ce allurar rigakafin corona na kamfanin AstraZeneca na da alfanu, a don haka kasashen nahiyar ka iya ci gaba da amfani da rigakafin.

Weltspiegel 18.03.2021 | Corona | AstraZeneca-Impfstoff
Hoto: Dado Ruvic/REUTERS

Bukatar kungiyar ta tarayyar Afirka na zuwa ne a lokacin da gomman kasashen nahiyar Turai suka dakatar da amfani da allurar saboda fargabar haifar da daskarewar jini da ake zargi take yi.

Nahiyar Afirka ita ma tuni ta bi sahun kasashen duniya da suka fara allurar rigakafin annobar corona, wanda kasashe da dama a nahiyar ke cin gajiyar tallafin rigakafin kamfanin AstraZeneca karkashin shirin nan na Hukumar Lafiya ta Duniya wato COVAX.