1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kungiyar AU ta dakatar da Guinea Conakry

September 10, 2021

Kungiyar Tarayyar Afirka wato AU, ta dakatar da kasar Guinea Conakry daga zama mamba a cikinta bayan kifar da gwamnatin Shugaba Alpha Conde.

Äthiopien Addis Abeba Außenminister vor dem Treffen der Afrikanischen Union
Hoto: picture-alliance/AA/M. W. Hailu

A wani sakon twitter, kungiyar ta AU ta ce daga yanzu Guinea Conakry ba za ta kasance cikin dukkanin harkokinta ba saboda kifar da gwamnati da dakarun kasar suka yi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai sojoji a Guinea Conakry suka murkushe gwamnatin kasar tare da kama hambararren Shugaba Alpha Conde.

Shi dai tsohon Shugaba Alpha Conde ya fuskanci suka saboda zargin sa da ake yi da mulkin kama karya.

Matakin kungiyar ta AU, ya zo ne kwana guda da ita ma kungiyar raya arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta dakatar da kasar kasancewa a cikin ta.

Kungiyar ta AU dai ta yi kiran sojojin Guinea Conkary da su gaggauta sakin Alpha Conde.