1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar AU ta dakatar da Sudan

Abdul-raheem Hassan
June 6, 2019

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afirka ta ce Sudan ba ta cikin kungiyar har sai ta kafa gwamnatin riko na farar hula. Matakin na da zimmar warware rikin da ke sanadiyar rayukan fararen hula.

Äthiopien Addis Abeba Moussa Faki
Hoto: picture-alliance/AA/M. W. Hailu

Matakin na zuwa ne a lokacin da likitoci a Sudan ke cewa adadin wadan da suka mutu a artabu da jami'an tsaro yayin zanga-zanga ya haura 100, amma hukumomin kwamitin mulkin soji ta karyata adadin.

Shugabannin kungiyoyin farare hula sun yi fatali da bukatar kwamitin mulkin soji na sake shiga tattaunawa domin samun dai-daito, inda kungiyoyin ke neman a hukunta wadan da suka aikata kisa.

Firaministan Habasha Abiy Ahmed na da niyyar sulhunta bangarorin da ke rikici da juna a Sudan, yayin da kungiyar Amnesty Intternational ta bukaci kasashen duniya su kawo dokin gaggawa kan rikin kasar da ke kashe fararen hula.

Tuni ma kasashe kamar Birtaniya da Majalisar Dinkin Duniya suka fara janye jami'ansu daga kasar Sudan, bayan da zaman kwamitin sulhu ya gaza samar da mafita kan halin da kasar ke ciki.