1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a zaben 'yan majalisun dokokin kasar Burundi

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 29, 2015

Kungiyar Tarayyar Afirka wato AU ta ce ba za ta halarci wajen zaben 'yan majalisun dokokin kasar Burundi da za a kada kuri'a a wannan Litinin din ba.

Zaben 'yan majalisa a Burundi
Zaben 'yan majalisa a BurundiHoto: Reuters/P. Nunes dos Santos

Kungiyar ta AU ta ce ba za ta sanya idanu a zaben ba ta la'akari da cewa akwai alamu da ke nuni da ba za a gudanar da zabe mai inganci kuma cikin adalci a Burundin ba. Matakin kungiyar ta AU ya biyo bayan bayyana aniyar kaurace wa zaben da 'yan adawar kasar suka yi, domin nuna adawarsu da yunkurin yin tazarce a karo na uku da Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi ya kafe a kai. Tuni dai kakakin majalisar wakilan kasar da shi ma ke adawa da yunkurin yin tazarcen na Nkurunziza ya tsere zuwa kasar Belgium. Tun da fari sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bukaci a jinkirta zabukan na Burundi biyo bayan kauracewar 'yan adawar, sai dai gwamnatin Nkurunziza ta yi watsi da wannan bukata.