1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Harm ta hallaka sojojin Chadi 24

Abdourahamane Hassane
August 5, 2021

Hukumomi Chadi sun sanar da cewar akalla sojojin gwamnatin kasar 24 'yan Boko Haram suka hallaka, yayin da wasu da dama suka yi batan dabo kasa ko sama kana wasu gomai suka jikkata.

Nigeria Region Borno Boko Haram
Hoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

Harin ya afku ne a tsibirin Tchoukou Telia da ke da nisan kilomita 190 daga arewa maso yammacin birnin Ndjamen babban birnin kasar. Wani kantoma a yankin na tafkin chadin Haki Djiddi, ya ce sojojin gwamnatin sun dawo daga sinitinri suna cikin hutawa kan hanya a sa'ilin da 'yan Boko Haram din suka afka musu. A halin da ake ciki gwamnatin Chadi ta ce ta tura karin sojoji a yankin domin bin sawun maharan.