1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabon

Kungiyar ECCAS ta dakatar da kasar Gabon

September 4, 2023

Jim kadan bayan rantsar da gwamnatin soja a Gabon, kungiyar raya kasashen tsakiyar Afirka ta dauki matakin ladabtar da sojojin kasar da suka kifar da gwamnatin Ali Bongo.

Shugaban gwamnatin soja a Gabon, Janar Brice Oligui Nguema
Shugaban gwamnatin soja a Gabon, Janar Brice NguemaHoto: AFP/Getty Images

Kungiyar raya ci gaban kasashen yankin tsakiyar Afirka ta ECCAS, ta dakatar da kasar Gabon daga zama mamba a cikinta, wani mataki da ke matsayin martani ga juyin mulki da aka yi a kasar.

A ranar 30 ga watan jiya na Agusta ne dai sojojin na Gabon suka hambare gwamnatin Shugaba Ali Bongo Ndemba.

Matakin dakatarwar na kuma zuwa ne, yayin da a yau Litinin shugaban gwamnatin soja a Gabon Janar Brice Nguema, wanda ya sha rantsuwar kama aiki ya yi alkawarin yafiya ga fursunonin siyasa da 'yan fafutika da hambararriyar gwamnati ta tsare a tsawon wa'adinta na mulki.

Janar Brice Nguema, ya ce gwamnatin da zai kafa nan gaba kadan, za ta yi wa daukacin mutanen da aka kama ahuwa, tare da duba yiwuwar dawowar wadanda aka tilasta wa yin gudun hijira.