Kungiyar EU ta amince da sharar fage don karbar kasar Bosnia a cikin ta.
November 21, 2005Ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar tarayyar Turai sun amince da tattaunawar sharar fage domin karbar kasar Bosnia a matsayin wakiliya a cikin kungiyar. Shawarar ta zo ne a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru goma da yarjejeniyar zaman lafiya da aka yiwa lakabi da Dayton accord wanda ya kawo karshen yaki na tsawon shekaru uku a yankin na Balkan. Bosnia ita ce kasa ta karshe daga tsohuwar kasar Yugoslavia da zata shiga sahun tattaunawa na dogon lokaci domin shiga kungiyar tarayyar tarayyar turan. Ministan kula harkokin kasashen ketzare na kungiyar tarayyar turan Javier Solana ya baiyana cewa shigar da kasashen yankin Balkan cikin kungiyar tarayyar turan zai taimaka wajen gano bakin zaren warware rikin Kosovo wanda ya ki ci yaki cinyewa.