1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

EU da China sun tattauna kan cin zarafi

September 15, 2020

Jamus ta yi murnar cewa EU da China sun daddale kan zargin gallaza wa kananan kabilu da 'yan fafutuka da ake zargin China da aikatawa. 

EU-China-Gipfel zu Markenschutz
Hoto: Reuters/Y. Herman

Jami'an kungiyar tarayyar Turai ta EU sun yi kira ga China da ta bude kofofin kasuwanci ta kuma gyara mu'amullarta da 'yan fafutuka. Wannan na zaman wani bangare na abubuwan da bangarori biyun suka tattauna a wurin taron bunkasa kasuwanci a tsakaninsu da ya gudana a ranar Litinin.

A taron wanda na bidiyo ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi murnar cewa a karshen taron sun tattauna abubuwa masu tsauri wadanda da farko ba su fahimci juna a kai ba musamman kan batun gallaza wa kananan kabilu da 'yan fafutuka da China ke yi.


Sai dai duk da dogon Turancin da EU da China suka fafata, a karshe sun amince su rinka cinikayyar kayan abinci a tsakaninsu.