1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

An nuna hotunan wasu daga Isra'ilawan da Hamas ke rike da su

Abdoulaye Mamane Amadou
April 27, 2024

Wasu 'yan Isra'ila biyu daga cikin wadanda kungiyar Hamas ke garkuwa da su sun bayyana a cikin wani faifan bidiyon da kungiyar ta fitar.

Hoto: Ilia Yefimovich/dpa/picture alliance

Kungiyar Hamas ta nuna hotunan wasu mutane biyu daga cikin Isra'ilawan da take garkuwa da su tun bayan harin da ta kaddamar a cikin kasar Isra'ila a watan Oktoban 2023.

An huna fuskokin Keith Siegel mai shekaru 64 da Omri Miran mai shekaru 47 ne a cikin wani faifan bidiyon da kungiyar ta fitar a ranar Asabar, kana tuni ma kwamitin dangi da 'yan uwan Isra'ilawan da Hamas din ke garkuwa da su suka tabbatar da mutane biyu.

Karin bayani: Isra'ila ta amince da murabus din Aharon Haliva

Duk da yake kungiyar Hamas ba ta bayyana ranar da aka nadi faifan bidiyon ba, an ji guda daga cikin Isra'ilawan na bayyana cewa tana hannun kungiyar ne fiye da kwanaki 200, sannan tana kira ga tattauna batun tsagaita buda wuta da kuma sakin wadanda ake garkuwa da su.

Karin bayani: Duniya ta bukaci kai zuciya nesa tsakanin Israila da Iran

Ko a tsakiyar wannan makon ma dai kungiyar Hamas da wasu manyan kasashe yammacin duniya ciki har da Jamus suka ayyana a matsayin ta 'yan ta'adda, ta wallafa wani faifan bidiyon matashi Ba-isra'ile Hersh Goldberg-Polin, mai shekaru 23 da take garkuwa da shi.