Kungiyar Hamas ta janye rundunar ta daga Zirin Gaza
May 26, 2006Talla
Kungiyar Hamas dake jan ragamar hukumar mulkin cin gashin kan Falasdinawa ta janye sabuwar rundunar ´yan sanda da ta girke a Zirin Gaza a makon da ya gabata. Hamas ta ce ta dauki wannan mataki ne don hana barkewar sabon fada tsakanin ´yan sandan ta da na magoya bayan kungiyar Fatah ta shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas.Wannan matakin ya zo ne a rana ta biyu a tarukan da ake yi da nufin yin sulhu tsakanin Hamas da Fatah, inda aka fi mayar da hankali akan batutuwan tsaro. Ko da ya ke Hamas ta lashe zaben ´yan majalisar dokoki da aka gudanar a cikin watan janeru, amma shugaba Mahmud Abbas ke iko da dakarun tsaro. Fadan na makon jiya a Zirin na Gaza yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 10.