1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Hamas ta yi watsi da shirin tattaunawa da Isra'ila

July 20, 2013

Kungiyar dake iko da Zirin Gaza ta mayar da martani ne bayan da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya sanar cewa sassan biyu za su koma kan teburin sulhu.

U.S. Secretary of State John Kerry (L) meets with Palestinian President Mahmoud Abbas at the Mukataa compound, in the West Bank city of Ramallah July 19, 2013. REUTERS/Mandel Ngan/Pool (WEST BANK (POLITICS)
Hoto: Reuters

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon, ya bayyana cewa ya ji dadi matuka da Isra'ila da Palasdinu suka yadda su sake zaunawa kan teburin shawara domin sasanta rikicin dake tsakaninsu. Ban Ki-Moon ya kuma yaba da kokarin da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya yi, na kokarin ganin ya shirya yadda Isra'ila da Palasdinawan za su zauna kan teburin shawarar. Sai dai a hannu guda kuma ana ci gaba da samun rarrabuwar kai tsakanin bangarori biyu na kungiyar Hamas da ke iko da yankin Zirin Gaza da kuma Fatah dake iko da gabar yammacin Kogin Jordan kan wannan batu. Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar Hamas dake zaman babbar jam'iyyar siyasa a kasar Palasdinu ta yi watsi da batun tattaunawarsu da Isra'ilan.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar

Edita: Mohammad Nasiru Awal