1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya kan kare hakki a Sudan

August 31, 2025

Yayin da rayukan fararen hula ke cikin garari a Sudan, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta kira Majalisar Dinkin Duniya kan bukatar kare mutane masu rauni daga hare-haren RSF.

'Yan hijira da rikici ya raba da sukuni a kasar Sudan
'Yan hijira da rikici ya raba da sukuni a kasar SudanHoto: AFP/Getty Images

Kungiyar kare hakkin bil Adam ta Human Rights Watch ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakan gaggawa domin kare fararen hula a yankunan yammacin Sudan daga hare-hare da kuma matsanancin yunwa da ake fuskanta a can.

Human Rights Watch din ta kuma roki Majalisar Dinkin Duniya da ta matsa wa rundunar RSF da ke jayayya da gwmanatin Sudan lamba, domin dakatar da hare-hare kan fararen hula, ciki har da cikin sansanonin 'yan gudun hijira na cikin gida.

Haka kuma, kungiyar ta bukaci bangarorin da ke rikici su dakatar da toshe hanyoyin kai agajin jinkai ga wadanda abin ya shafa.

Tun watan Afrilu na shekarar 2024, dakarun RSF suka kewaye garin El Fasher, lamarin da ya hana kai agaji da na bukatu na yau da kullum.