1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar IS na kara samun mayaka

Lateefa Mustapha Ja'afarSeptember 17, 2014

Kwararru a kan lamuran tsaro sun bayyana cewa kungiyar 'yan ta'addan IS na kara samun magoya baya da mayakan sa kai.

Hoto: picture alliance/abaca

Tun bayan da Amirka ta kaddamar da kai hare-hare a kan kungiyar IS ta masu kaifin kishin addini da ta addabi Siriya da Iraki, kungiyar ke kara samun magoya baya da ma sababbin mayaka. Shugaban FBI ta Amirkan James Comey ya ce kungiyar na amfani da kafafen yada labarai na zamani wajen bayyana akidojinta wanda kuma ke taimaka mata gaya gurin samun magoya baya da sababbin mayaka. Shi kuwa shugaban cibiyar yaki da ta'addanci ta Amirkan Matthew Olsen cewa ya yi a yanzu haka kungiyar ta IS na da mayaka kimanin dubu 20 zuwa dubu 31. Olsen ya ce kungiyar ta IS na yada manufofinta ta hanyar yin Farfaganda mai karfin gaske da ta zarta irn wacce sauran kungiyoyin ta'adda na duniya ke yi. Wannan bayani dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amirka ta tashi tsaye domin yakar kungiyar ta IS ko ta halin kaka, inda ta ke zawarcin wasu kasashe domin su shiga a fafata da su.