1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

IS ta dauki alhakin harin Iran

Suleiman Babayo AH
January 5, 2024

Gwamnatin Iran ta bayyana cafke wasu da ake zargi da hannu wajen kai harin da ya halaka kimanin mutane 100, yayin da tsagerun kungiyar IS suka dauki alhakin kai harin.

Harin Kerman na Iran
Harin Kerman na IranHoto: Fars/ZUMA Press Wire via picture alliance

Gwamnatin Iran ta bayyana kama wasu da ake zargi da hannu wajen kai tagwayen bama-bamai a wannan mako da suka halaka kimanin mutane 100. Harin da tuni tsagerun kungiyar IS masu kaifin kishin addinin Islama suka dauki alhakin kai wa. Ministan ciki na kasar Ahmad Vahidi ya shaida wa kofofin yada labaran kasar cewa akwai mutane da aka kama wadanda ake zargi suna da hannu kan harin.

A ranar Laraba da ta gabata aka kai harin kusa da kabarin tsohon kwamdann sojan Iran Qassem Soleimani wanda dakarun Amirka suka halaka kimanin shekaru hudu da suka gabata.