Kungiyar IS ta sace mutane da dama a Siriya
August 7, 2015Talla
Mutanen dai da suka hada da 'yan sunna 170 da kuma Kiristoci 60 an kame su ne bayan wani bincike da 'yan kungiyar suka aiwatar a gidajansu, inda suke zarginsu da hada baki da gwamnatin ta Siriya a cewar Rami Abdel Rahmane darektan kungiyar da ke kula da sa Ido kan hakokin Bi'adama a kasar ta Siriya.
Sai dai daga na shi bangare Arch-Bishop Matta al-Khoury, da ke birnin Damascus, ya ce basu da wannan labari, amma kuma ya ce suna da masaniyar cewa, bayan da 'yan jihadin na IS suka shiga wannan gari, sun hana kowa fita daga gidansa, domin al'ummar garin ta kasance garkuwa garesu daga harin dakarun gwamnatin ta Siriya.