1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar IS ta yi ikrarin harin Sri Lanka

Abdullahi Tanko Bala
April 23, 2019

Kungiyar IS ta yi ikrarin cewa mambobinta ne suka kai hare haren kunar bakin wake a Sri Lanka da ya hallaka mutane fiye da 300 yayin bukukuwan Easter a ranar Lahadi.

Police officers work at the scene at St. Sebastian Catholic Church in Negombo
Hoto: Reuters/A. Perawongmetha

Jami'an tsaro sun kama mutane fiye da 40 dangane da harin na Sri Lanka ciki har da direban wata mota da ake zargi yan kunar bakin waken sun yi amfani da ita. Hakannan kuma an tsare wani mai gidan da wasu daga cikin mutanen da ake zargi suke zaune.

Hare haren shida da aka kai a kusan lokaci guda, an kai su ne kan wasu manyan otel guda uku da wani coci a Colombo babban birnin kasar da kuma wasu coci guda biyu a biranen kasar ta Sri Lanka a lokacin bukukuwan Easter a ranar Lahadi.

Hukumomi sun yi imanin cewa wata kungiyar Tawfik Jama'ath ce ta kai harin tare da hadin kai da wasu kungiyoyin yan ta'adda na kasashen ketare.

Ministan tsaron Sri Lanka Ruwan Wijerwardene ya shaidawa majalisar dokoki a wannanTalatar cewa harin ramuwar gayya ce ga harin da aka kai kan musulmi a wani masallaci a Christchurch a kasar New Zealnad, sai dai bai yi wani karin haske ba.