Kungiyar jihadi ta JNIM da dauki alhakin kai hari a Bamako
September 17, 2024Kungiyar masu jihadi ta JNIM mai alaka da Al-Qaida da tauki alhakin harin da aka kai a filin jirgin sama da kuma wani sansanin soji a Bamako babban birnin kasar Mali tare da yin ikirarin halaka mutane da dama da kuma lalata kadarori.
Sai dai Rundunar sojin Malin ta sanar da cewa ta dakile wani yunkurin 'yan ta'adda na kutsawa wata makarantar horas da jami'an tsaro da ke tsakiyar birnin Bamako, a yayin wani hari da ba a cika ganin irinsa ba a babban birnin kasar.
Shaidu sun ce sun jiyo karar harbe-harbe da kuma fashewar abubuwa da kimanin karfe biyar na safayar Talata a daidai lokacin sallar Asuba, sannan kuma an hango hayaki ya turnike sararin samaniya a kusa da filin jiragen sama na birnin.
A cikin sanarwar da ta fidda, rundunar sojin Mali ta ce bayan harin da bai yi nasara ba tana ci gaba da gudanar da bincike, sai dai amma an ce an samu jami'an tsaro biyu da suka jikkata kamar yadda makusantasu suka tabbatar wa manema labarai.
Duk da cewa an samu lafawar al'amura, amma an rufe filin jirgin saman Bamako na dan lokaci, sannan kungiyoyi kasa-kasa sun bukaci ma'aikatansu da su takaita tafiye-tafiye.