Rasha da kasashen Larabawa na neman tsagaita wuta a Gaza
December 20, 2023Taron da ke gudana a karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Morocco Nasser Bourita, ya samu halartar ministan harkokin wajen Rasha Lavrov da jami'an diflomasiyya na kungiyar kasashen Larabawa mai mambobi 22, da ya kuma ya mayar da hankali kan rikicin Gaza.
A wannan Larabar ce ake saran kwamitin sulhu na MDD zai kada kuri'a kan wani kuduri da ke neman a dakatar da rikicin, kamar yadda wasu majiyoyin diflomasiyya suka shaida.
Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan dubu 20, akasari mata da kananan yara, a cewar ma'aikatar lafiyar yankin na Falasdinu da ke karkashin ikon Hamas.
A ranar 7 ga watan Oktoba, mayakan Hamas sun kai wani hari da ba a taba ganin irinsa ba a kan Isra'ila daga Gaza, inda suka kashe mutane kusan 1,200, galibi fararen hula, a cewar alkaluman hukumomin na Isra'ila.