1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar kasashen larabawa za ta kori Siriya daga cikin kungiyar

October 17, 2011

Ci-gaba da tursasawa faran fula da gwamnatin Bashard Al-Assad ta ke yi ya fara janyo bacin ran kungiyar kasashen larabawan wacce ke shirin daukar mataki

Bashar Assad shugaban kasar SiriyaHoto: dapd

Ministocin harkokin waje na kungiyar kasashen larabawa na gudanar da wani taron a birnin alkahira na kasar Masar,domin duba yiwar kwarrar kasar Siriya daga cikin kungiyar saboda tursasawar da sojojin shugaba Bashar Al Assad suke yi akan masu gudanar da zanga zangar neman canjin mulki.

Wani babban jamin diflomasiya na kungiyar ya gayawa manema labarai cewa taron zai yanke shawarar na gaba, sai dai kasashen da dama na kungiyar na nuna rashin amincewar su na kwarrar Siriya, wanda har yanzu gwamnatin kasar bata ce ufan ba akan batun.kungiyar dai ta tilasawa gwamnatin kasar ta Siriya da ta tsayar da ranar da zata fara janye dakarunta daga cikin garuruwa daban daban inda ta jijibg su domin kawo karshen zubar da jinin da ake ci gaba da samu.Majalisar Dinkin duniya ta ce kawo yanzu mutane kusan dubu ukku suka rasa rayukansu a cikin yamutsin na kasar ta Siriya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita Umaru Aliyu