Kungiyar AES ta cika shekaru biyu
September 16, 2025
A kwana a tashi shekaru biyu kenan da kasashen na Nijar, Mali da Burkina Faso suka kafa wannan kungiya ta AES da nufin hada karfi da karfe wajen yaki da ta'addanci da sauran matsaloli na tsaro kafin daga bisani su rikidar da kungiyar tasu zuwa hadaka wani kawance da nufin karfafa huldarsu a fannoni kamar na Siyasa, Diplomasiyya, tattalin arziki da dai sauransu. Kuma Malam Ismael Mohamed na Kungiyar Debout Niger ya ce ba karamin alkahiri ba ne Nijar ta samu a tsawon wadannan shekaru biyu na zama a cikin kungiyar ta AES.
To sai dai wasu 'yan Nijar na ganin babu wani ci gaban da kasar ta samu a tsawon wadannan shekaru biyu, hasalima kasashen biyu na ci da gumin gasar Nijar ne kawai a cikin tafiyar. Malam Siraji Issa na kungiyar Mojen, na daga cikin masu irin wannan ra'ayi.
To amma Malam Roufa'i Sani mai sharhi kann harkokin yau da kullum a Nijar na ganin duk da abubuwan ci gaba da kungiyar ta AES ta haifar ga kasashen uku, akwai wasu batutuwan da ke bukatar gyara a cikin tafiyar kungiyar.
A hakumance dai babu wani biki na musamman da gwamnatin kasar Nijar ta shirya domin raya ranar zagayowar shekaru biyu da kafuwar kungiyar ta AES, bikin da ya zo a daidai loakcin da kungiyoyin ‚yan ta'adda ke kara zafafa hare-harensu kan sojoji da fararan hula a cikin kasashen uku.