1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

'Yan gudun hijirar Sudan sun cika Sudan ta Kudu

Abdourahamane Hassane
December 23, 2024

Kungiyar Medecin Sans Frontiere MSF ta ce Sudan ta Kudu na fama da kwararrar 'yan gudun hijirar daga Sudan, makobciyarta.

Hoto: Sally Hayden/SOPA Images/Sipa USA/picture alliance

 Dubban mutane daga Sudan na shiga kasar wadanda suka ke tserewa zafafan fadan, in ji kungiyar likitocin.A cewar kungiyar, a kowace rana  sama da mutane dubu biyar ke tsallaka kan iyaka zuwa Sudan ta Kudu,wadda ita ma ke fama da tashe-tashen hankula na yau da kullum, baya ga iftalin yanayi.Tun daga watan Afrilun na shekara ta 2023, yaki ya barke a kasar Sudan, wanda ya hada da sojoji karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhane, da dakarun Rapid Support Forces (FSR) na tsohon mataimakinsa, Janar Mohamed Hamdane Daglo. Kawo yanzu  dubun-dubatar mutane suka mutu, yayin da wasu sama  miliyan 11 suka rasa  matsugunansu.